< 以赛亚书 16 >

1 你们当将羊羔奉给那地掌权的, 从西拉往旷野,送到锡安城的山。
Ku aiko da raguna a matsayin haraji ga mai mulkin ƙasar, daga Sela a hamada, zuwa dutsen Diyar Sihiyona.
2 摩押的居民在亚嫩渡口, 必像游飞的鸟,如拆窝的雏。
Kamar tsuntsaye masu firiya da aka kora daga sheƙa, haka matan Mowab suke a kogunan Arnon.
3 求你献谋略,行公平, 使你的影子在午间如黑夜, 隐藏被赶散的人,不可显露逃民。
“Ku ba mu shawara, ku yanke shawara. Ku mai da inuwarku kamar dare, a tsakar rana. Ku ɓoye masu gudun hijira, kada ku bashe masu neman mafaka.
4 求你容我这被赶散的人和你同居。 至于摩押,求你作他的隐密处, 脱离灭命者的面。 勒索人的归于无有, 毁灭的事止息了, 欺压人的从国中除灭了,
Ku bar Mowabawa masu gudun hijira su zauna tare da ku; ku zama mafakarsu daga mai neman hallaka su.” Mai danniya zai zo ga ƙarshe hallaka kuma za tă daina; masu lalatar da ƙasa za su kare
5 必有宝座因慈爱坚立; 必有一位诚诚实实坐在其上, 在大卫帐幕中施行审判, 寻求公平,速行公义。
Da ƙauna za a kafa kursiyi; da aminci mutum zai zauna a kansa, wani daga gidan Dawuda, wani wanda ta shari’antawa yakan nuna gaskiya ya hanzarta yin adalci.
6 我们听说摩押人骄傲, 是极其骄傲; 听说他狂妄、骄傲、忿怒; 他夸大的话是虚空的。
Mun ji fariyar Mowab, mun ji yawan fariyarta da girmankanta, fariyarta da reninta, amma taƙamarsu ta banza ce.
7 因此,摩押人必为摩押哀号; 人人都要哀号。 你们摩押人要为吉珥·哈列设的葡萄饼哀叹, 极其忧伤。
Saboda haka Mowabawa za su yi kuka mai zafi, za su yi kuka mai zafi tare saboda Mowab. Ku yi makoki ku kuma yi baƙin ciki saboda ƙosai da kuka riƙa ci a Kir Hareset.
8 因为希实本的田地 和西比玛的葡萄树都衰残了。 列国的君主折断其上美好的枝子; 这枝子长到雅谢延到旷野, 嫩枝向外探出,直探过盐海。
Gonakin Heshbon sun bushe, inabin Sibma ma haka. Masu mulkin al’ummai sun tattake inabi mafi kyau, waɗanda suka taɓa yaɗuwa zuwa Yazer suka bazu ta wajen hamada. Tohonsu sun buɗu suka kai har teku.
9 因此,我要为西比玛的葡萄树哀哭, 与雅谢人哀哭一样。 希实本、以利亚利啊, 我要以眼泪浇灌你; 因为有交战呐喊的声音 临到你夏天的果子, 并你收割的庄稼。
Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka, saboda inabin Sibma. Ya Heshbon, ya Eleyale, na cika ku da hawaye! Sowa ta murna a kanku saboda’ya’yan itatuwanku da suka nuna da kuma girbinku sun ɓace.
10 从肥美的田中夺去了欢喜快乐; 在葡萄园里必无歌唱,也无欢呼的声音。 踹酒的在酒榨中不得踹出酒来; 我使他欢呼的声音止息。
An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu’ya’ya; babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi; babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi, gama na kawo ƙarshen yin sowa.
11 因此,我心腹为摩押哀鸣如琴; 我心肠为吉珥·哈列设也是如此。
Zuciyata tana makoki saboda Mowab kamar garaya, na yi baƙin ciki saboda Kir Hareset.
12 摩押人朝见的时候,在高处疲乏,又到他圣所祈祷,也不蒙应允。
Sa’ad Mowab ta bayyana a masujadar bisa tudu, tana gajiyar da kanta ne kawai; sa’ad da ta tafi wurin tsafinta don tă yi addu’a, babu wani amfani.
13 这是耶和华从前论摩押的话。
Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya riga ya yi game da Mowab.
14 但现在耶和华说:“三年之内,照雇工的年数,摩押的荣耀与他的群众必被藐视,余剩的人甚少无几。”
Amma yanzu Ubangiji ya ce, “Cikin shekara uku, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, haka za a mai da daraja da kuma dukan yawan mutanen Mowab abin reni, daga ɗumbun mutanenta,’yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”

< 以赛亚书 16 >