< 1 Kings 17 >

1 Elijah the Tishbite, who was one of the settlers of Gilead, said to Ahab, “As the LORD, the God of Israel, lives, before whom I stand, there shall not be dew nor rain these years, but according to my word.”
To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.”
2 Then the LORD’s word came to him, saying,
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce,
3 “Go away from here, turn eastward, and hide yourself by the brook Cherith, that is before the Jordan.
“Ka bar nan, ka nufi wajajen gabas, ka ɓuya a Rafin Kerit, gabas da Urdun.
4 You shall drink from the brook. I have commanded the ravens to feed you there.”
Za ka sha daga rafin, zan kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”
5 So he went and did according to the LORD’s word, for he went and lived by the brook Cherith that is before the Jordan.
Saboda haka sai Iliya ya yi abin da Ubangiji ya faɗa masa. Ya tafi Rafin Kerit, gabas da Urdun, ya zauna a can.
6 The ravens brought him bread and meat in the morning, and bread and meat in the evening; and he drank from the brook.
Hankaki suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da yamma, ya kuma sha daga rafin.
7 After a while, the brook dried up, because there was no rain in the land.
Ana nan sai rafin ya bushe saboda ba a yi ruwan sama a ƙasar ba.
8 The LORD’s word came to him, saying,
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya cewa,
9 “Arise, go to Zarephath, which belongs to Sidon, and stay there. Behold, I have commanded a widow there to sustain you.”
“Je ka, nan take, zuwa Zarefat na Sidon, ka zauna a can. Na umarci wata gwauruwa a can tă ciyar da kai.”
10 So he arose and went to Zarephath; and when he came to the gate of the city, behold, a widow was there gathering sticks. He called to her and said, “Please get me a little water in a jar, that I may drink.”
Saboda haka sai ya tafi Zarefat. Sa’ad da ya isa ƙofar gari, sai ga wata gwauruwa tana tattara’yan itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa a tulu don in sha.”
11 As she was going to get it, he called to her and said, “Please bring me a morsel of bread in your hand.”
Da ta kama hanya za tă tafi tă kawo, sai ya sāke kiranta ya ce, “Ina roƙonki, ki kuma kawo mini ɗan abinci.”
12 She said, “As the LORD your God lives, I do not have anything baked, but only a handful of meal in a jar and a little oil in a jar. Behold, I am gathering two sticks, that I may go in and bake it for me and my son, that we may eat it, and die.”
Sai ta ce masa, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da wani abinci, sai dai ɗan gari hannu guda a tulu, da kuma ɗan mai a kwalaba. Ina tattara’yan itacen nan ne don in kai gida in yi abinci wa kaina da ɗana, don mu ci, mu mutu.”
13 Elijah said to her, “Do not be afraid. Go and do as you have said; but make me a little cake from it first, and bring it out to me, and afterward make some for you and for your son.
Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Ki tafi gida, ki yi yadda kika ce. Amma da farko ki yi mini’yar wainar burodi daga abin da kike da shi ki kawo mini, sa’an nan ki yi wani abu wa kanki da kuma ɗanki.
14 For the LORD, the God of Israel, says, ‘The jar of meal will not run out, and the jar of oil will not fail, until the day that the LORD sends rain on the earth.’”
Gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Tulun garin ba zai ƙare ba, kwalabar man kuma ba zai bushe ba sai ranar da Ubangiji ya bayar da ruwan sama a ƙasar.’”
15 She went and did according to the saying of Elijah; and she, he, and her household ate many days.
Sai ta tafi, ta yi yadda Iliya ya faɗa mata. Saboda haka aka kasance da abinci kowace rana wa Iliya da kuma don macen da iyalinta.
16 The jar of meal did not run out and the jar of oil did not fail, according to the LORD’s word, which he spoke by Elijah.
Gama tulun garin bai ƙare ba, kwalabar man kuma bai bushe ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Iliya.
17 After these things, the son of the woman, the mistress of the house, became sick; and his sickness was so severe that there was no breath left in him.
Ana nan sai ɗan matan, wato, gwauruwan nan ya fara ciwo. Ciwon ya ƙara muni, daga ƙarshe sai ya daina numfashi.
18 She said to Elijah, “What have I to do with you, you man of God? You have come to me to bring my sin to memory, and to kill my son!”
Sai ta ce wa Iliya, “Mutumin Allah, yaya haka? Ka zo ne domin ka nuna wa Allah zunubaina, ka kuma jawo mutuwar ɗana?”
19 He said to her, “Give me your son.” He took him out of her bosom, and carried him up into the room where he stayed, and laid him on his own bed.
Iliya ya ce, “Ki miƙa mini ɗanki.” Sai ya ɗauke shi daga hannuwanta, ya kai shi ɗakin sama inda yake zama, ya kwantar da shi a gadonsa.
20 He cried to the LORD and said, “LORD my God, have you also brought evil on the widow with whom I am staying, by killing her son?”
Sa’an nan ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wannan masifa a kan gwauruwan nan? Kai ka ce in zauna tare da ita, ga shi yanzu ɗanta ya mutu.”
21 He stretched himself on the child three times, and cried to the LORD and said, “LORD my God, please let this child’s soul come into him again.”
Sai ya kwanta, ya miƙe kansa a kan yaron sau uku, ya kuma yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka mai da ran yaron nan!”
22 The LORD listened to the voice of Elijah; and the soul of the child came into him again, and he revived.
Ubangiji kuwa ya ji kukan Iliya, sai ran yaron ya dawo masa, ya kuma rayu.
23 Elijah took the child and brought him down out of the room into the house, and delivered him to his mother; and Elijah said, “Behold, your son lives.”
Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga ɗakin sama zuwa cikin gida. Ya ba da shi ga mahaifiyarsa, ya ce, “Duba, ɗanki yana da rai!”
24 The woman said to Elijah, “Now I know that you are a man of God, and that the LORD’s word in your mouth is truth.”
Sai matar ta ce wa Iliya, “Yanzu na san cewa kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuma yana magana ta wurinka.”

< 1 Kings 17 >