< Jeremiah 3 >

1 “They say, ‘If a man puts away his wife, and she goes from him, and becomes another man’s, should he return to her again?’ Would not that land be greatly polluted? But you have played the prostitute with many lovers; yet return again to me,” says the LORD.
“In mutum ya saki matarsa ta kuwa bar shi ta auri wani mutum, zai iya komo da ita kuma? Ƙasar ba za tă ƙazantu gaba ɗaya ba? Amma kun yi rayuwa kamar karuwa da masoya masu yawa yanzu za ki komo wurina?” In ji Ubangiji.
2 “Lift up your eyes to the bare heights, and see! Where have you not been lain with? You have sat waiting for them by the road, as an Arabian in the wilderness. You have polluted the land with your prostitution and with your wickedness.
“Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani. Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba? A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki, kin zauna kamar makiyayi a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da karuwancinki da muguntarki.
3 Therefore the showers have been withheld and there has been no latter rain; yet you have had a prostitute’s forehead and you refused to be ashamed.
Saboda haka an hana yayyafi, kuma babu ruwan bazara da ya sauka. Duk da haka kina da irin kallon da karuwa takan yi; kin ƙi ki ji kunya.
4 Will you not from this time cry to me, ‘My Father, you are the guide of my youth!’?
Yanzu ba kin kira ni, ‘Mahaifina, abokina daga ƙuruciyata ba,
5 “‘Will he retain his anger forever? Will he keep it to the end?’ Behold, you have spoken and have done evil things, and have had your way.”
kullum za ka riƙa fushi? Hasalarka za tă ci gaba har abada ne?’ Haka kike magana, amma kina aikata dukan muguntar da kika iya yi.”
6 Moreover, the LORD said to me in the days of Josiah the king, “Have you seen that which backsliding Israel has done? She has gone up on every high mountain and under every green tree, and has played the prostitute there.
A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can.
7 I said after she had done all these things, ‘She will return to me;’ but she did not return, and her treacherous sister Judah saw it.
Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za tă komo wurina amma ba tă yi haka ba,’yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani.
8 I saw when, for this very cause, that backsliding Israel had committed adultery, I had put her away and given her a certificate of divorce, yet treacherous Judah, her sister, had no fear, but she also went and played the prostitute.
Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina.
9 Because she took her prostitution lightly, the land was polluted, and she committed adultery with stones and with wood.
Domin fasikancin Isra’ila bai yi tasiri gare ta ba, sai ta ƙazantar da ƙasar ta kuma yi zina da dutse da kuma itace.
10 Yet for all this her treacherous sister, Judah, has not returned to me with her whole heart, but only in pretense,” says the LORD.
Duk da wannan duka, Yahuda’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce,” in ji Ubangiji.
11 The LORD said to me, “Backsliding Israel has shown herself more righteous than treacherous Judah.
Ubangiji ya ce mini, “Isra’ila marar bangaskiya ta fi Yahuda marar aminci.
12 Go, and proclaim these words toward the north, and say, ‘Return, you backsliding Israel,’ says the LORD; ‘I will not look in anger on you, for I am merciful,’ says the LORD. ‘I will not keep anger forever.
Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa, “‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba, gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.
13 Only acknowledge your iniquity, that you have transgressed against the LORD your God, and have scattered your ways to the strangers under every green tree, and you have not obeyed my voice,’” says the LORD.
Ki dai yarda da laifinki kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye, kin watsar da alheranki ga baƙin alloli a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’” in ji Ubangiji.
14 “Return, backsliding children,” says the LORD, “for I am a husband to you. I will take one of you from a city, and two from a family, and I will bring you to Zion.
“Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona.
15 I will give you shepherds according to my heart, who will feed you with knowledge and understanding.
Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi.
16 It will come to pass, when you are multiplied and increased in the land in those days,” says the LORD, “they will no longer say, ‘the ark of the LORD’s covenant!’ It will not come to mind. They will not remember it. They will not miss it, nor will another be made.
A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.
17 At that time they will call Jerusalem ‘The LORD’s Throne;’ and all the nations will be gathered to it, to the LORD’s name, to Jerusalem. They will no longer walk after the stubbornness of their evil heart.
A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba.
18 In those days the house of Judah will walk with the house of Israel, and they will come together out of the land of the north to the land that I gave for an inheritance to your fathers.
A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo.
19 “But I said, ‘How I desire to put you among the children, and give you a pleasant land, a goodly heritage of the armies of the nations!’ and I said, ‘You shall call me “My Father”, and shall not turn away from following me.’
“Ni kaina na faɗa, “‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar’ya’yana maza in ba ki ƙasa mai daɗi, gādo mafi kyau da wata al’umma.’ Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’ ba za ki ƙara rabuwa da bina ba.
20 “Surely as a wife treacherously departs from her husband, so you have dealt treacherously with me, house of Israel,” says the LORD.
Amma kamar mace marar aminci ga mijinta, haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji.
21 A voice is heard on the bare heights, the weeping and the petitions of the children of Israel; because they have perverted their way, they have forgotten the LORD their God.
An ji kuka a filayen tuddai, kuka da roƙon mutanen Isra’ila, domin sun lalace hanyoyinsu sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu.
22 Return, you backsliding children, and I will heal your backsliding. “Behold, we have come to you; for you are the LORD our God.
“Ku komo, mutane marasa bangaskiya; zan warkar da ku daga ja da bayanku.” “I, za mu zo wurinka, gama kai ne Ubangiji Allahnmu.
23 Truly help from the hills, the tumult on the mountains, is in vain. Truly the salvation of Israel is in the LORD our God.
Tabbatacce hayaniyar bin gumaka a kan tuddai da duwatsu banza ne; tabbatacce a wurin Ubangiji Allahnmu ne akwai ceton Isra’ila.
24 But the shameful thing has devoured the labor of our fathers from our youth, their flocks and their herds, their sons and their daughters.
Daga ƙuruciyarmu allolin kunya sun cinye mu amfanin wahalar kakanninmu garkunan tumakinsu da na awakinsu, yaransu maza da mata.
25 Let us lie down in our shame, and let our confusion cover us; for we have sinned against the LORD our God, we and our fathers, from our youth even to this day. We have not obeyed the LORD our God’s voice.”
Bari mu kwanta mu sha kunya, bari kuma kunyarmu ta rufe mu. Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi, da mu da kakanninmu; daga ƙuruciyarmu har yă zuwa yau ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba.”

< Jeremiah 3 >