< لوقا 13 >

در آن وقت بعضی آمده او را از جلیلیانی خبر دادند که پیلاطس خون ایشان را با قربانی های ایشان آمیخته بود. ۱ 1
A lokacin, wadansu mutane suka gaya masa game da galilawa wadanda Bilatus ya gauraye jininsu da hadayunsu.
عیسی در جواب ایشان گفت: «آیا گمان می‌برید که این جلیلیان گناهکارتر بودند از سایر سکنه جلیل ازاین‌رو که چنین زحمات دیدند؟ ۲ 2
Sai Yesu ya amsa masu yace “Kuna tsammani wadannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawan zunubi ne, da suka sha azaba haka?
نی، بلکه به شما می‌گویم اگر توبه نکنید، همگی شماهمچنین هلاک خواهید شد. ۳ 3
A'a, ina gaya maku. In ba ku tuba ba, dukanku za ku halaka kamarsu.
یا آن هجده نفری که برج در سلوام بر ایشان افتاده ایشان را هلاک کرد، گمان می‌برید که از جمیع مردمان ساکن اورشلیم، خطاکارتر بودند؟ ۴ 4
Ko kuwa mutane goma sha takwas din nan da suna Siluwam wadanda hasumiya ta fado a kansu ta kashe su, kuna tsamani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?
حاشا، بلکه شما رامی گویم که اگر توبه نکنید همگی شما همچنین هلاک خواهید شد.» ۵ 5
Ina gaya maku ba haka bane. Amma duk wanda ya ki tuba, dukanku za su hallaka”
پس این مثل را آورد که «شخصی درخت انجیری در تاکستان خود غرس نمود و چون آمدتا میوه از آن بجوید، چیزی نیافت. ۶ 6
Yesu ya fada wannan misali, “Wani mutum yana da baure wanda ya shuka a garkar inabinsa sai ya zo neman 'ya'yan itacen amma bai samu ba.
پس به باغبان گفت اینک سه سال است می‌آیم که از این درخت انجیر میوه بطلبم و نمی یابم، آن را ببر چرا زمین رانیز باطل سازد. ۷ 7
Sai mutumin ya ce wa mai kula da garkar, “ka ga, shekara uku kenan nake zuwa neman 'ya'yan wannan baure, amma ban samu ba. A sare shi. Yaya za a bar shi ya tsare wurin a banza?
در جواب وی گفت، ای آقاامسال هم آن را مهلت ده تا گردش را کنده کودبریزم، ۸ 8
Sai mai lura da garkar ya amsa yace, 'Ka dan ba shi lokaci kadan in yi masa kaftu in zuba masa taki.
پس اگر ثمر آورد والا بعد از آن، آن راببر.» ۹ 9
In yayi 'ya'ya shekara mai zuwa to, amma in bai yi 'ya'ya ba sai a sare shi!”'
و روز سبت در یکی از کنایس تعلیم می‌داد. ۱۰ 10
Wata rana Yesu yana koyarwa a wata majami' a ran Asabaci.
و اینک زنی که مدت هجده سال روح ضعف می‌داشت و منحنی شده ابد نمی توانست راست بایستد، در آنجا بود. ۱۱ 11
Sai, ga wata mace a wurin shekarunta goma sha takwas tana da mugun ruhu, duk ta tankware, ba ta iya mikewa.
چون عیسی او را دید وی را خوانده گفت: «ای زن از ضعف خودخلاص شو.» ۱۲ 12
Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, an warkar da ke daga wannan cuta.”
و دست های خود را بر وی گذارد که در ساعت راست شده، خدا را تمجیدنمود. ۱۳ 13
Sai Yesu ya dora hannunsa a kanta, nan da nan sai ta mike a tsaye ta fara daukaka Allah.
آنگاه رئیس کنیسه غضب نمود، از آنروکه عیسی او را در سبت شفا داد. پس به مردم توجه نموده، گفت: «شش روز است که باید کاربکنید در آنها آمده شفا یابید، نه در روزسبت.» ۱۴ 14
Amma shugaban majami'a yayi fushi domin Yesu yayi warkarwa a ranar Asabaci. Sai shugaban ya amsa yace wa jama'a, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo domin a warkar da ku amma ba ranar Asabaci ba.”
خداوند در جواب او گفت: «ای ریاکار، آیاهر یکی از شما در روز سبت گاو یا الاغ خود را ازآخور باز کرده بیرون نمی برد تا سیرآبش کند؟ ۱۵ 15
Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe kowannenku ba ya kwance Jakinsa ko Sa daga turkensa ya kai shi banruwa ran Asabaci?
و این زنی که دختر ابراهیم است و شیطان او رامدت هجده سال تا به حال بسته بود، نمی بایست او را در روز سبت از این بند رها نمود؟» ۱۶ 16
Ashe wannan 'yar gidan Ibrahim, wanda shaidan ya daure ta shekara goma sha takwas, wato ba za a iya kwance ta a ranar Asabaci kenan ba?
وچون این را بگفت همه مخالفان او خجل گردیدندو جمیع آن گروه شاد شدند، بسبب همه کارهای بزرگ که از وی صادر می‌گشت. ۱۷ 17
Da ya fada wadannan abubuwa, dukansu da suka yi adawa da shi suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwa masu daraja da yayi.
پس گفت: «ملکوت خدا چه چیز را می‌ماندو آن را به کدام شی تشبیه نمایم. ۱۸ 18
Sai Yesu ya ce, “Yaya za a misalta mulkin Allah, kuma da me zan kwatanta shi?
دانه خردلی راماند که شخصی گرفته در باغ خود کاشت، پس رویید و درخت بزرگ گردید، بحدی که مرغان هوا آمده در شاخه هایش آشیانه گرفتند.» ۱۹ 19
Yananan kamar kwayar mastad, wanda wani mutum ya dauka ya jefa ta a lambunsa, ta kuma yi girma ta zama gagarumin itace, har tsuntsaye suka yi shekarsu a rassanta.”
باز‌گفت: «برای ملکوت خدا چه مثل آورم؟ ۲۰ 20
Ya sake cewa, “Da me zan kwatanta mulkin Allah?
خمیرمایه‌ای را می‌ماند که زنی گرفته در سه پیمانه آرد پنهان ساخت تا همه مخمرشد.» ۲۱ 21
Yana kamar yisti wanda wata mace ta dauka ta cuda da mudu uku na garin alkama don ya kumburar da shi.”
و در شهرها و دهات گشته، تعلیم می‌داد وبه سوی اورشلیم سفر می‌کرد، ۲۲ 22
Yesu ya ziyarci kowanne birni da kauye, a hanyar sa ta zuwa Urushalima yana koyar da su.
که شخصی به وی گفت: «ای خداوند آیا کم هستند که نجات یابند؟» او به ایشان گفت: ۲۳ 23
Sai wani ya ce masa, “Ubangiji, wadanda za su sami ceto kadan ne?” Sai ya ce masu,
«جد و جهد کنید تااز در تنگ داخل شوید. زیرا که به شما می‌گویم بسیاری طلب دخول خواهند کرد و نخواهندتوانست. ۲۴ 24
“Ku yi kokari ku shiga ta matsatsiyar kofa, domin na ce maku, mutane dayawa za su nemi shiga amma ba za su iya shiga ba.
بعد از آنکه صاحب‌خانه برخیزد ودر را ببندد و شما بیرون ایستاده در را کوبیدن آغاز کنید و گویید خداوندا خداوندا برای ما بازکن. آنگاه وی در جواب خواهد گفت شما رانمی شناسم که از کجا هستید. ۲۵ 25
In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe kofa, sannan za ku tsaya a waje kuna kwankwasa kofar kuna cewa, 'Ubangiji, Ubangiji, bari mu shiga ciki'. Sai ya amsa yace maku, 'Ni ban san ku ba ko daga ina ku ka fito.'
در آن وقت خواهید گفت که در حضور تو خوردیم وآشامیدیم و در کوچه های ما تعلیم دادی. ۲۶ 26
Sannan za ku ce, 'Mun ci mun sha a gabanka, ka kuma yi koyarwa a kan titunanmu.'
بازخواهد گفت، به شما می‌گویم که شما رانمی شناسم از کجا هستید؟ ای همه بدکاران از من دور شوید. ۲۷ 27
Amma zai amsa ya ce, “Ina gaya maku, ban san ko daga ina ku ka fito ba, ku tafi daga wurina, dukanku masu aikata mugunta!'
در آنجا گریه و فشار دندان خواهدبود، چون ابراهیم واسحق و یعقوب و جمیع انبیارا در ملکوت خدا بینید و خود را بیرون افکنده یابید ۲۸ 28
Za a yi kuka da cizon hakora a lokacin da kun ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu da dukan annabawa a mulkin Allah amma ku-za a jefar da ku waje.
و از مشرق و مغرب و شمال و جنوب آمده در ملکوت خدا خواهند نشست. ۲۹ 29
Za su zo daga gabas, yamma, kudu, da arewa, za su ci a teburin abinci a mulkin Allah.
و اینک آخرین هستند که اولین خواهند بود و اولین که آخرین خواهند بود.» ۳۰ 30
Ku san da wannan, na karshe za su zama na farko, na farko kuma za su zama na karshe.”
در همان روز چند نفر از فریسیان آمده به وی گفتند: «دور شو و از اینجا برو زیرا که هیرودیس می‌خواهد تو را به قتل رساند.» ۳۱ 31
Nan take, wadansu farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ka tafi daga nan domin Hirudus yana so ya kashe ka.”
ایشان را گفت: «بروید و به آن روباه گوییداینک امروز و فردا دیوها را بیرون می‌کنم ومریضان را صحت می‌بخشم و در روز سوم کامل خواهم شد. ۳۲ 32
Yesu ya ce, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, 'Duba, na fitar da aljanu, ina warkarwa yau da gobe, kuma a rana ta uku kuwa zan gama aiki na.'
لیکن می‌باید امروز و فردا و پس‌فردا راه روم، زیرا که محال است نبی بیرون ازاورشلیم کشته شود. ۳۳ 33
Ko da kaka, dole ne in ci gaba da tafiyata yau, da gobe, da kuma jibi, don bai dace a kashe annabi nesa da Urushalima ba.
‌ای اورشلیم، ای اورشلیم که قاتل انبیا و سنگسار کننده مرسلین خودهستی، چند کرت خواستم اطفال تو را جمع کنم، چنانکه مرغ جوجه های خویش را زیر بالهای خود می‌گیرد و نخواستید. ۳۴ 34
Urushalima, Urushalima masu kisan annabawa, masu jifan wadanda aka aiko gare ku. Sau nawa ne ina so in tattara 'ya'yanki kamar yadda kaza take tattara 'ya'yanta a cikin fukafukanta, amma ba ki so wannan ba.
اینک خانه شمابرای شما خراب گذاشته می‌شود و به شمامی گویم که مرا دیگر نخواهید دید تا وقتی آیدکه گویید مبارک است او که به نام خداوندمی آید.» ۳۵ 35
Duba, an yashe gidanki. Ina kwa gaya maku ba za ku kara ganina ba sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.'”

< لوقا 13 >