< 1 Тимофію 4 >

1 Дух же явно глаголе, що в останнї часи відступлять декотрі од віри, слухаючи духів лестивих і наук бісових,
To Ruhu ya fada a fili cewa, a zamanin karshe wadansu mutane za su kauce daga bangaskiya, su mai da hankalin su ga ruhohi masu rudi, da koyarwar aljannu,
2 в лицемірстві брехливих, запеклих у совістї своїй,
cikin karya da munafunci. Lamirinsu zai yi kanta.
3 що боронять женитись (і велять вдержуватись) од їжи, що Бог створив на їду з подякою вірним і познавшим правду.
Za su haramta aure da karbar abincin da Allah ya halitta, domin su raba da godiya a cikin wadanda suka bada gaskiya suka kuma san gaskiyar.
4 Бо всяке створіннє Боже добре і шщо не гидке, коди з подякою приймаємо;
Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau. Domin duk abin da muka karba da godiya, bai kamata mu ki shi ba.
5 осьвячуєть ся бо словом Божим і молитвою.
Gama an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da addu'a.
6 Се все нагадуючи браттю, будеш добрий служитель Ісуса Христа, годований словами віри і доброю наукою, котрій послїдував єси.
Idan ka tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa za ka zama bawan kirki na Almasihu. Domin ana gina ka ne ta wurin maganar bangaskiya da kuma kyakkyawar koyarwa wadda ka bi.
7 Скверних же і бабських байок цурай ся, а привчай себе до благочестя.
Amma ka guji labaran almara wadanda tsofaffin mata ke so. Maimakon haka sai ka hori kanka cikin bin Allah.
8 Тілесна бо вправа мало корисна, а благочестє корисне на все, маючи обітницю життя нинішнього і будучого
Domin horon jiki ya na da amfani kadan. Amma horon kai cikin bin Allah yana da amfani ga dukkan abubuwa. Gama a cikinsa akwai alkawari domin wannan rayuwar da kuma rayuwa mai zuwa.
9 Вірне слово і всякого приняття достойне.
Maganan nan amintacciyace ta isa a karbe ta dungum.
10 На се бо і трудимось і ганять нас, що вповали на Бога живого, котрий єсть Спаситель усіх людей, а найбільш вірних.
Dalilin da ya sa kenan mu ke aiki tukuru. Domin muna sa bege ga Allah mai rai, mai ceton dukkan mutane, musamman masu ba da gaskiya.
11 Звіщай се і навчай.
Ka yi shela ka kuma koyar da wadannan abubuwa.
12 Ніхто ж нехай молодістю твоєю не гордує; а будь взором для вірних, у слові, у життю, у любові, у дусі, у чистоті.
Kada ka yarda kowa ya rena kuruciyarka. Maimakon haka, ka zama abin koyi ga dukkan masubi: a furci, hali, kauna, aminci da kuma tsarki.
13 Доки прийду, пильнуй читання, утїшення, науки.
Har sai na zo, ka himmatu da yin karatu, da wa'azi, da kuma koyarwa.
14 Не занедбай твого дарування, котре дано тобі пророцтвом, з положеннєм рук сьвященства.
Kada ka yi sakaci da baiwar da ka ke da ita wadda aka baka ta wurin anabci sa'ad da dattawa suka dibiya maka hannayensu.
15 Про се дбай, в сьому пробувай, щоб успіх твій явен був у всїх.
Ka kula da wadannan abubuwa. Ka himmatu a cikinsu. Domin ci gabanka ya zama sananne a idanun kowa.
16 Пильнуй себе і науки; пробувай у сьому; се бо роблячи, і сам спасеш ся і ті, що слухають тебе.
Ka kula da kanka da kuma koyawarka. Ci gaba a cikinsu. Domin ta yin haka ne za ka ceci kanka da masu sauraronka.

< 1 Тимофію 4 >